Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Mourinho ya nemi a kira shi da sunan “The Unique One”

Kocin Real Madrid, Jose Mourinho yace daga yanzu yafi bukatar a kira shi da Sunan “The Unique One” maimakon “The Special One” saboda nasarorin da ya samu a aikin horar da ‘Yan wasa a kungiyoyin daban daban a Turai a wata hira da ya yi da gidan Telebijin na Channel Sic a kasar Portugal.

José Mourinho. kocin Real Madrid a spain
José Mourinho. kocin Real Madrid a spain Reuters
Talla

Mourinho ya lashe kofin league a kasar Portugal a FC Porto sannan ya lashe Premier a Chelsea tare da lashe Seria A a Italia da kuma La liga a Spain.

A cewar Mourinho yanzu duniya tana kiran shi ne da sunan “The Only One” amma yafi bukatar a kira shi da Sunan “The Unique One”.

A karshen makon nan ne dai kungiyoyin Spain za su fara fafatawa a La liga, kuma har yanzu adawa ce tsakanin Barcelona da Real Madrid.

A kaka da ta gabata Real Madrid ce ta lashe kofin gasar da tazarar maki 8 tsakninta da Barcelona, kuma ko yanzu ga alamu a bana kungiyoyin biyu ne za su ci gaba da hamayya a Jagorancin Teburin gasar.

Babu wani sauyi a tawagar Real Madrid da Barcelona, ‘Yan wasan Barcelona da suka haramtawa Real Madrid lashe kofin sau uku a jere su ne dai za su sake fafata da ‘Yan wasan Mourinho da suka samu nasarar lashe kofin a karon farko karkashin jagorancin shi.

Sai dai Tito Vilanova shi ne zai jagoranci Barcelona ba Guardiola ba bana kamar yadda adawar take a da, yanzu wata sabuwar adawa ce za’a girka a Spain.

Vilanova shi ne mataimakin Guardiola a shekaru hudu da Guardiola ya kwashe a Barcelona inda suka lashe kofi 14. Don haka adawar ba sabuwa bace.

Akwai dan wasa Jordi Alba da Vilanova ya saya daga Valencia akan kudi Euro Miliyan 14. Amma kuma Vilanova yana neman yanzu wanda zai maye gurbin Seidou Keita na Mali wanda ya koma buga wasa a China.

Akwai ‘Yan wasa da Barcelona ke shawarar saye domin maye gurbin Kaita wadanda suka hada da Javi Martinez na Athletic Bilbao da kuma Alex Song na Arsenal.

Yanzu dai akwai wasan Super Cup tsakanin Barcelona da Real Madrid a karshen watan Agusta, anan ne kuma zamu iya gane yadda adawa zata kasance tsakanin Mourinho da Vilanova
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.