Isa ga babban shafi
Tennis

Roland Garros: Federer da Djokovic zasu kara a zagayen kusa da karshe

A gasar Roland Garros ta French Open da ake gudanarwa a Faransa, Roger Federer da Novak Djokovic zasu sake haduwa a zagyen kusa da karshe, bayan sun sha da kyar a zagayen Quarter Final.

Novak Djokovic a lokacin da yake murnar doke  Andreas Seppi a gasar Roland Garros.
Novak Djokovic a lokacin da yake murnar doke Andreas Seppi a gasar Roland Garros. REUTERS/Nir Elias
Talla

A jiya ne Federer ya samu nasar Doke Juan Martin del Potro, kuma Novak Djokovic ya yi kokarin doke Jo-Wilfried Tsonga na Faransa a Quarter Final.

A bara Djokovic da Federer sun taba karawa a zagayen kusa da karshe a gasar Roland Garros, sai dai Roger Federer ne ya samu nasarar doke Djokovic wanda ya buga wasanni 43 ba tare da samun galabar shi ba a bara.

Amma kuma tun a lokacin, Djokovic ya lashe kofuna 26 a jere da suka hada da Wimbledon da Us Open a bara hadi da Austalian Open a watan Janairu.

A Tarihin Rolland Garros, tsakanin Djokovic da Federer babu wanda ya taba samun galabar Rafeal Nadal wanda ya lashe wasanni 49 ba tare da samun galabar shi ba illa wasa daya da Robin Soderling na Sweden da ya samu sa’ar shi a zagyen na hudu a shekarar 2009.

A yau laraba ne Andy Murray na Birtaniya zai kara da David Ferer na Spain a Quarter Final. Kuma dan wasan ya bayyana fargabar iya ficewa gasar saboda rauni a bayanshi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.