Isa ga babban shafi
Tennis

Azarenka ta fice French Open, Djokovic da federer sun tsallake

Jarumar wasan Tennis ta duniya, Victoria Azarenka ta fice gasar French Open ta Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa bayan ta sha kashi hannun Dominika ‘yar kasar Slovakia.

Victoria Azarenka ta Belarus a lokacin da take fafatwa a gasar Australian Open
Victoria Azarenka ta Belarus a lokacin da take fafatwa a gasar Australian Open Reuters
Talla

A bangaren maza, Novak Djokovic da Roger Federer sun sha da kyar a jiya Lahadi kafin su tsallake zuwa zagayen Quarter Final.

Novak Djokovic ya yi kokarin farfadowa ne kafin ya doke Andreas Seppi dan kasar Itaila.
Roger Federer wanda ya taba lashe gasar a shekarar 2009 ya samu nasar doke David Goffin ne dan kasar Belgium.

A zagayen Qauter Final federer zai kara ne tsakanin shi da Juan Martin Del Potro na Argentina ko Thomas Berdych na Jamhuriyyar Czech

A yau Litinin ne Rafel Nadal zai kara da Juan Monaco na Argentina a zagaye na hudu. Bayan dan wasan ya yi bukin cika shekaru 26 na haihuwa a ranar Lahadi.
.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.