Djokovic zai fara haskawa a gasar Roland Garros
A yau litinin ne aka shiga kwana na biyu a gasar Tennis ta Roland Garros a Faransa. A yau ne kuma Novak Djokovic zai fara haskawa a gasar inda zai kara da Potito Starace dan kasar Italia a zagayen Farko.
Wallafawa ranar:
Novak Djokovic dai ya lashe kofin Wimbledon da US Open da Australian Open amma bai taba buga wasan karshe ba a French Open. Domin sau uku yana shan kashi a zagayen kusa da karshe.
Roger Federer kuma wanda ya taba lashe Roland Garros a shekarar 2009, a yau Litinin ne, shi ma zai fara haskawa inda zai kara da Tobias Kamke dan kasar Jamus.
A fafatawar farko a jiya Lahadi Jo-Wilfried Tsonga na Faransa ya samu nasarar doke Andrey Kuznetsov na Rasha.
A bangaren mata kuma, mai rike da kofin gasar Li Na ‘Yar kasar China a yau zata kece raini da Sorana ‘yar kasar Romania.
Victoria Azarenka kuma jarumar Tennis a Duniya zata kara ne da Alberta Brianti ‘yar kasar Italia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu