Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Neymar na Brazil ba zai bar Santos ba sai zuwa 2014

Neymar Matashin dan wasan Brazil wanda zai yi bukin cika shekaru 20 a watan gobe, yace zai ci gaba da rayuwarsa a kungiyar shi ta Santos har zuwa watan Yulin shekarar 2014, bayan kammala gasar cin kofin Duniya a Brazil.

Neymar, dan wasan kungiyar Santos ta Brazil
Neymar, dan wasan kungiyar Santos ta Brazil REUTERS/Kim Kyung-Hoon
Talla

Neymar ya bayyana haka ne lokacin da ya kai ziyara Montevideo babban birnin kasar Uruguay, domin karbar kyautar gwarzon dan wasan yankin Amurka.

A cewar Neymar ba zai bar Santos ba har sai kwangilar shi ta kawo karshe da Santos a shekarar 2014 bayan sabunta kwangilar a watan Nuwamban bara.

Neymar ya zira yawan kwallaye 81 cikin wasannu 159 daya buga a Santos.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.