An rufe katafariyar hasumiyar Paris kan yajin aikin ma'aikata
An rufe katafariyar hasumiyar nan ta Eiffel Tower da ke birnin Paris na kasar Faransa kwanaki hudu a jere, sakamakon yajin aikin da ma’aikatan wurin yawon bude idon ke yi kan rashin kulawar da ta dace da mahukunta ke baiwa wurin.
Wallafawa ranar:
Jaridar Le Monde ta kasar ta ruwaito cewa, yajin aikin shi ne na biyu cikin watanni biyu kan irin wannan dalili, wanda na wannan karo ya fara da zanga-zangar lumana a ranar Litinin.
Ma’aikatan na zargin hukumar da ke kula da wurin yawon shakatawar da gazawa, suna bukatar a kara yawan kudin da ake kashewa na kula tare da gudanar da hasumiyar domin ci gaba da kasancewa cikin kyakyawar yanayi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu