Isa ga babban shafi

Real Madrid na cikin tattaunawar dauko Mbappe daga Paris Saint Germain

Real Madrid na cikin tattaunawa da dan wasan gaba na Paris Saint Germain, Kylian Mbappé a game da sauya sheka zuwa kungiyar a karshen wannan kaka, kuma sun yi amannar cewa za a cimma yarjejeniya nan ba da jimawa ba, kamar yadda wasu majiyoyi suka bayyana.

Dan wasan gaba na PSG, Kylian Mbappé.
Dan wasan gaba na PSG, Kylian Mbappé. AFP - MIGUEL MEDINA
Talla

A makon da ya gabata ne aka samu labarin cewa Mbappé ya shaida wa kungiyarsa ta PSG aniyarsa ta barinta a lokacin da kwantiraginsa zai kare a karshen wannan kaka, bayan da ya yanke shawarar cewa makomarsa tana Real Madrid.

A cikin watan da ya gabata, Madrid ta gabatar da tayi a hukumance a kan dan wasan na kasar Faransa, a yayin da PSG ke ci gaba da fatan za ta rinjayi dan wasan ya ci gaba da zama a kungiyar.

Majiyoyi sun ce a halin da ake ciki, Real Madrid na fatan kammala kulla yarjejeniya da dan wasan nan gaba kadan, sai dai har yanzu ba a kai ga sanya hannu a kan kwantiragi ba, saboda akwai wasu batutuwa da suka kamata a cimma matsaya a kai.

Kwallaye 32 ne Mbappe ya ci a wannan kaka gaba daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.