Isa ga babban shafi

Ba ni da tabbacin kungiyar da zan koma bayan rabuwa da PSG - Mbappe

Dan wasan gaba na PSG Kylian Mbappe ya ce har yanzu bai kammala tsayar da shawara kan makomarsa ba, domin kuwa bai tabbatar da kungiyar da zai koma da taka leda ba, dai dai lokacin da kwantiraginsa ke karewa da kungiyar ta birnin Paris.

Kyaftin din PSG Kylian Mbappé.
Kyaftin din PSG Kylian Mbappé. REUTERS - SARAH MEYSSONNIER
Talla

Mbappe wanda shi ne kyaftin din tawagar kwallon kafar Faransa da kungiyarsa ta PSG mai doka gasar lig 1, yanzu haka akwai kungiyoyin da ke zwarcinsa, sai dai an fi alakanta shi da Real Madrid lura da cewa sau biyu kenan bangarorin na tattaunawa kan yiwuwar komawarsu Santiago Barnabeu amma ana samun matsala.

Mbappe mai shekaru 25 tun a watan Yunin bara ne ya tabbatarwa PSG cewa ba zai sake amincewa da tsawaita  wa’adin zamansa a Parc des Princes har na watanni 12 kamar yadda kungiyar ta bukata ba.

Da ya ke zantawa da manema labarai bayan nasararsu ta lallasa Toulous da kwallaye 2 da 1, Mbappe ya ce a bana ya na da cikakken kwarin gwiwar iya yin gaban kansa wajen yanke hukunci kan makomar tasa amma har yanzu bai tsayar da kungiyar da zai koma taka leda ba.

A shekarar 2017 ne PSG ta sayo Mbappe daga Monaco kan farashin yuro miliyan 180 kuma tun a kakar wasa ta 2022 ne ya kammala wa’adinsa amma ya sake tsawaitawa da shekaru 2 bayan bukatar hakan hatta daga shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.