Isa ga babban shafi

Ina da tabbacin Mbappe zai lashe kyautar Ballon d'Or sau da dama - Enrique

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta PSG Luis Enrique, ya ce ya na da yakinin dan wasan gaba na kungiyar Kylian Mbappe zai lashe kyautar Ballon d'Or, kwana uku bayan da dan wasan dan asalin Faransa ya kare a mataki na uku, bayan Messi da Haaland da suka yi na daya da kuma na biyu.

Dan wasan gaba na tawagat Faransa da kuma kungiyar PSG Kylian Mbappé .
Dan wasan gaba na tawagat Faransa da kuma kungiyar PSG Kylian Mbappé . AFP - FRANCK FIFE
Talla

A lokacin da ya ke gabatar da taron manema labarai a Alhamis din nan Enrique, ya ce kafin mutum ya samu damar lashe wannan kyauta, ya na bukatar bada gudunmuwa ga kungiyarsa da kuma kasarsa, kuma Mbappe na iya kokarinsa a wannan bangaren.

"A nan PSG muna kokarin samun nasara sosai, kuma dan wasa kamar Kylian, na tabbata zai lashe Ballon d'Or da dama."

Kyaftin din Argentina Lionel Messi da ya bar kungiyar PSG a farkon kakar wasan bana, wanda ya taikawa kasar wajen lashe gasar lashe kofin duniya da ake yi a Qatar ne ya samu nasarar lashe kyautar, wacce aka bayar a ranar Litinin din da ta gabataa birnin Paris.

Dan wasan Manchester City Erling Haaland ne kuma yazo na biyu, yayin da Kylian Mbappe da ya taimakawa kasarsa Faransa zuwa wasan karshe a gasar lashe kofin duniya ya kare a mataki na uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.