Isa ga babban shafi

Messi ya lashe kyautar Ballon d'Or karo na takwas

Tauraron kwallon kafar Argentina da a yanzu ke kungiyar Inter Miami a Amurka, Lionel Messi, ya lashe kyautar gwarzon duniya ta Ballon d’Or karo na takwas.

Lionel Messi dauke da kyautar Ballon d'Or karo na takwas a birnin Paris. 30 Oktoba, 2023.
Lionel Messi dauke da kyautar Ballon d'Or karo na takwas a birnin Paris. 30 Oktoba, 2023. AFP - FRANCK FIFE
Talla

Messi ya kafa wannan tarihi ne bayan gudunmawar da ya bai wa kasarsa Argentina wajen lashe gasar cin kofin duniya da kasar Qatar ta karbi bakunci a shekarar bara.

A halin yanzu Messi ya zarta duk wani dan kwallon kafa da karin kyautar Ballon d’Or uku, yayin da Cristiano Ronaldo ke biye da shi bayan lashe kyautar sau 5.

A karon farko cikin shekaru 20, Ronaldo bai samu shiga cikin jerin sunayen ‘yan wasan da aka zaba domin tantance  wanda zai lalshe kyautar gwarzon dan kwallon kafar na duniya ba.

A wannan karon dai Kylian Mbappe ne ya zo na biyu a bikin ba da kyautar ta Ballon d’Or yayin da Erling Haaland ya zo na uku.

Erling Haaland
Erling Haaland REUTERS - STEPHANIE LECOCQ

Baya ga kasancewa na uku, Haaland ya lashe kyautar yi wa sauran takwarorinsa zarra wajen cin kwallaye, la’akari da cewar jimillar 52 ya ci wa Manchester City a kakar  wasan da ta gabata, abinda ya taimaka wa kungiyar tasa lashe kofunan gasar Zakarun Turai, da na Premier da kuma na FA.

A bangaren masu tsaron raga, golan Argentina da ke cikin tawagar da ta lashe gasar kofin duniya, Emiliano Martinez da ke kungiyar Aston Villa ne ya lashe kyautar gwarzon mai tsaron ragar na duniya.

Jude Bellingham
Jude Bellingham © LUSA - HUGO DELGADO

Dan wasan Real Madrid Jude Bellingham da shi ma ya shiga jerin ‘yan wasan da aka karrrama yayin bikin da ya gudana a daren Litinin din da ta gabata a birnin Paris, ya lashe kyautar zama gwarzon dan wasa ta matasa ‘yan kasa da shekaru 21.

Vinicius Junior
Vinicius Junior REUTERS - PABLO MORANO

Shi kuwa Vinicius Junior takwaran Bellingham a dai  kungiyar ta Real Madrid, kyautar Socrates ya lashe, saboda jajircewarsa wajen taimakon marasa karfi, bayan da ya  kafa gidauniyar gina makarantu, tare  da bunkasa samar da ilimi a yankunan marasa galihu da ke kasarsa Brazil.

Bayan karbar kyautar ta Socrates, Vinicius Junior ya sha alwashin ci gaba da yakar dabi'ar masu wariyar launin fata a duniyar kwallon kafa.

Ya zuwa yanzu dai dan wasan ya shafe kusan shekaru biyu yana fuskantar cin zarafin wariyar launin fata yayin buga wasannin gasar La Liga, lamarin da ya sanya manyan 'yan wasa tsaffi  da na yanzu da kuma jami'an kwallon kafa, har ma da gwamnatin kasarsa yin tir da musgunawa Vinicius.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.