Jerin 'yan wasa 30 da za a zabi zakaran Ballon d'Or na bana
An fitar da jerin sunayen ‘yan wasa 30 da za su fafata wajen takarar neman lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara ta Ballon d’Or, jerin sunayen da ke fita karon farko cikin shekaru 20 ba tare da sunan tauraron Portugal ba wato Cristiano Ronaldo.
Wallafawa ranar:
Dan wasan gaba na Najeriya da Napoli Victor Osimhen ya shiga cikin jerin ‘yan wasan da aka zaba a matsayin wadanda za su yi wannan takara ta Ballon d’Or lamarin da ya mayar da shi dan Najeriya na farko da aka zaba domin lashe kyautar bangaren maza tun bayan shekarar 1999.
Masu shirya kyautar, wato French Football, sun tabbatar da zaben Osimhen ne a daren jiya Laraba, sakamakon rawar ganin da ya taka a kakar wasan da ta wuce, inda ya taimakawa kungiyarsa ta Italiya lashe kyautar Scudetto ta farko cikin shekaru 33.
Osimhen ya zura kwallaye 25 a gasar lig a kakar da ta wuce, inda ya doke Lautaro Martinez na Inter Milan da Rafael Leao na AC Milan wajen samun kyautar gwarzon dan wasan gaba a Seria A.
Ya kuma taimaka wa kungiyar ta kai wasan daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta UEFA, kuma ya taka rawar gani wajen taimakawa Super Eagles ta Najeriya samun tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na wannan shekara da aka jinkirta.
Wannan matakin ya bai wa dan wasan mai shekaru 24 lambar yabo a matsayin dan Afrika na farko da ya jagoranci jerin 'yan wasan Seria A, yayinda ya goge tarihin George Weah na yawan kwallayen da dan Afirka ya ci a gasar ta Italiya.
'Yan wasa 30 da za su fafata don lashe Ballon d'Or
Julian Alvarez
Nicolo Barella
Jude Bellingham
Karim Benzema
Yassine Bounou
Kevin De Bruyne
Ruben Dias
Ilkay Gundogan
Antoine Griezmann
Josko Gvardiol
Erling Haaland
Harry Kane
Khvicha Kvaratskhelia
Robert Lewandowski
Randal Kolo Muani
Emiliano Martinez ne adam wata
Lautaro Martinez
Kylian Mbappe
Lionel Messi
Kim Min Ka
Luka Modric
Jamal Musala
Martin Odegaard
Andre Onana
Victor Osimhen
Rodri
Bukayo Saka
Mohammed Salah
Bernardo Silva
Vinicius Jr
Manchester City ce ta fi kowacce kungiya yawan 'yan wasan da suka shiga wannan jeri, yayinda Afrika ke da wakilcin 'yan wasa 4.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu