Isa ga babban shafi

Mutane uku sun jikkata sakamakon harin wuka a tashar jirgin kasa ta Paris

A birnin Paris na kasar Faransa wani harin wuka ya raunata mutane uku a yau Asabar a tashar jirgin kasa ta Gare de Lyon da ke birnin.'yan sanda sun sanar da cafke wanda ya kai wannan hari.

Jirgin kasa a tashar Gare de Lyon
Jirgin kasa a tashar Gare de Lyon © Wikimedia commons
Talla

Mutumin da aka tsare, wanda ba a bayyana asalin kasarsa ba, ya kai farmaki ne da misalin karfe 8:00 a tashar da ke jigilar jiragen kasa na cikin gida da kuma wadanda ke zuwa Switzerland da Italiya.

‘Yan sanda sun ce mutum daya ya samu munanan raunuka yayin da wasu biyu suka samu sauki.

Tashar jiragen kasa na Gare de Lyon
Tashar jiragen kasa na Gare de Lyon AFP - GEOFFROY VAN DER HASSELT

Rahotanni daga birnin na Paris na nuni cewa,mutumin da yan Sanda suka kama na dauke da takardun tukin mota na kasar Italia,yan lokuta da kama mutumin ,yan sanda sun karfafa matakan tsaro a wannan wuri da ake samun  yawaitar matafiya zuwa cikin kasar da waje.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.