Isa ga babban shafi

Fushin manoma na kara girma a Faransa da Tarayyar Turai

Shugaban jam'iyyar masu ra’ayin rikau a Faransa (LR) Eric Ciotti ya na mai fatan ganin Gwamnati ta biya manoma mafi karancin kudin na Euro 1,500 a kowane wata, dan siyasar na fadar haka ne yayin wata hira da jaridar JDD.

Zanga-zangar manoman Faransa
Zanga-zangar manoman Faransa REUTERS - BENOIT TESSIER
Talla

Eric Ciotti ya ce "Dole ne mu samar da tsarin tallafin kudi ga manoman da ke kasa da kangin talauci, bai dace manomi ya samu kasa da Euro 1,500 a kowane wata."

Manoma a kasar Faransa
Manoma a kasar Faransa REUTERS - NACHO DOCE

Jagoran 'yancin ya yi imanin cewa za a iya samar da irin wannan matakin "ta hanyar sanya takunkumi mai karfi ga masu rarrabawa wadanda ba su mutunta dokar da ta ba da tabbacin mafi ƙarancin farashi don samar da noma" da kuma cire "wasu ka’idoji a matsayin taimako ga manoman.

 

Ya kuma yi kira da a kawo karshen yarjejeniyoyin ciniki cikin 'yanci da kuma haramta shigo da kayayyaki daga kasashen da ba sa mutunta ka'idojin zamantakewa da muhalli kamar Faransa.

Shugaban Faransa lokacin ganawa da manoman Faransa
Shugaban Faransa lokacin ganawa da manoman Faransa REUTERS - POOL

A yau lahadi ake kyautata zaton Firaminista Gabriel Attal wanda ya ba da sanarwar matakai da yawa a ranar Jumma'a da suka hada da soke karuwar dizal da kuma tabbatar da cewa Faransa ba za ta amince da shi ba kamar yadda yake kan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin EU da kasashen Latin Amurka.

 

Shugabanin kungiyoyin Manoman Faransa Arnaud Rousseau daga FNSEA da Arnaud Gaillotbayan ganawa da Firaministan Faransa
Shugabanin kungiyoyin Manoman Faransa Arnaud Rousseau daga FNSEA da Arnaud Gaillotbayan ganawa da Firaministan Faransa AFP - DIMITAR DILKOFF

Manoma sun dage wasu shingen kan manyan tituna, amma sun yi alkawarin saka matsin lamba kama daga ranar Litinin.

 

Firaministan Faransa Gabriel Attal ya isa yankin Parçay-Meslay, da Indre-et-Loire, wata alama ta nunawa manoman cewa hukumomi sun damu ainun da halin da suke ciki yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.