Isa ga babban shafi

Majalisar dokokin Faransa ta goyi bayan dokar zubar da ciki

FARANSA – Majalisar wakilan Faransa ta amince da gagarumin rinjaye shirin baiwa mata damar zubar da ciki a matsayin  dokar kasa kamar yadda shugaban kasa Emmanuel Macron ya yi alkawari.

Wasu matan dake zanga zangar goyan bayan dokar zubar da ciki a Paris
Wasu matan dake zanga zangar goyan bayan dokar zubar da ciki a Paris AFP - THOMAS SAMSON
Talla

‘Yan majalisun dokokin Faransa 493 suka amince da kudirin sabuwar dokar, cikin su harda magoya bayan jam’iyyar shugaba Emmanuel Macron, yayin da wasu 30 suka ki goyan bayan kudirin.

Ministan shari’ar kasar Eric Dupond-Moretti ya bayyana cewar majalisar ta dauki matakan da suka dace wajen kare martabar mata.

Shugaba Macron da wasu ‘yan majalisar dokokin kasar suka bukaci samar da dokar wadda aka kwashe lokaci ana tafka shari’a a kanta tun daga shekarar 1974, domin ganin an sanya ta cikin kundin tsarin mulki bayan da kotun kolin Amurka a shekarar 2022 ta kawo karshen takaddama a kan irin wannan dokar.

Samar da sauyi a kan kundin tsarin mulki a Faransa na bukatar gudanar da kuri’ar jin ra’ayin jama’a ko kuma amincewar kashi 3 bisa 5 na daukacin ‘yan majalisun kasar.

Ana saran majalisar dattawa ta fara mahawara a kan kudirin dokar daga ranar 28 ga watan Fabarairu mai zuwa.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin ‘yan majalisar dattawan na adawa da kudirin, abinda ake ganin cewar zai haifar da mahawara sosai a tsakanin su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.