Isa ga babban shafi

Mutum daya ya mutu wasu sun samu rauni a harin wukar da wani kai a Paris

Mutum daya ya rasa ransa, sannan wasu biyu sun jikkata bayan da wani mai tsa-tsauran ra’ayin addini ya kai wa wasu masu tafiya a kafa hari da wuka a tsakiyar birnin Paris a yammacin jiya Asabar, kamar yadda ministan harkokin cikin gidan Faransa Gerald Darmanin ya tabbatar.

Wani jami'in dan sanda a wurin da aka kai hari da wuka a birnin Paris na Faransa.
Wani jami'in dan sanda a wurin da aka kai hari da wuka a birnin Paris na Faransa. AFP - DIMITAR DILKOFF
Talla

A lokacin da ya ke tsokaci game da lamarin a shafinsa na X da akafi sani da Twitter, ministan ya tabbatar da cewar wanda ake zargin ya kai wa wasu masu yawon shakatawa hari ne, inda ya kashe daya da kuma raunata biyu daga cikinsu.

"Yan sanda sun kama wani maharin da ya kai hari kan masu wucewa a birnin Paris, a kusa da Quai de Grenelle. Mutum daya ya mutu, wanda kuma suka jikkata jami'an kwana-kwana na Paris sun basu musu magani. Don Allah a kauracewa wurin."

Wanda ake zargi ya yi suna wajen tsatsauran ra’ayin addinin Islama, sannan ya na fama da matsalar kwa-kwalwa, inda ya ce al’amarin da ke faru a Gaza ne ya tunzurashi wajen aikata hakan.

A cewar ministan harkokin cikin gidan Faransa Darmanin, wanda ya rasa ransa sanadiyar harin dan asalin Jamus ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.