Isa ga babban shafi

Kotun Faransa ta fara sauraren shari'ar matasa 6 kan kisan Samuel Paty

Wasu matasa 6 sun gurfana gaban kotun Faransa yau Litinin, don amsa tuhuma kan kisan malamin tarihi Samuel Paty da aka fillewa kai cikin shekarar 2020, a zaman shari’ar na farko cikin zama biyu da aka tsara game da batun wanda ya tayar da hankalin kasar.

Malamin Tarihi Samuel Paty da matashi dan Chechenia ya kashe saboda batanci ga fiyayyen halitta.
Malamin Tarihi Samuel Paty da matashi dan Chechenia ya kashe saboda batanci ga fiyayyen halitta. AP - Lewis Joly
Talla

Malamin tarihi Samuel Paty mai shekaru 47 an daba masa wuka ne gabanin fille masa kai lokacin da ya ke tsaka da tafiya a gefen hanya gab da makarantar da ya ke koyarwa da ke birnin Paris.

Tun a wancan lokacin jami’an tsaron Paris suka kashe matashin da ya aikata kisan wanda aka bayyana sunanshi da Abdoullakh Anzorov dan Chechenia mai shekaru 18 da ke gudun hijira a kasar ta Faransa.

Matashin dai ya kashe Paty ne bayan wasu sakonnin dandalin sadarwa da suka nuna yadda malamin ke nunawa dalibansa hoton barkwancin da mujallar Charlie Hebdo ta yi game da fiyayyen halitta Annabin rahma tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi.

Paty ya yi amfani da mujallar ta Charlie Hebdo ne wajen gwada misali kan ‘yancin fadin albarkacin baki wanda ke karkashin dokokin Faransa, dokokin da suka sahale batanci ga addinai.

Kisan na Party na zuwa ne mako guda bayan jaridar ta Charlie Hebdo ta fitar da zanen barkwancin makamancin wanda suka wallafa a shekarar 2015 da ya janyo harin da ya hallaka ma’aikatan mujallar 12.

Ko a watan jiya ma, matashi Mohammed Moguchkov ya hallaka malami Dominique Bernard a yankin Arras da ke arewacin Faransa lamarin da tuni yankinsa da ke cikin kasar Rasha mai rinjayen mabiya addinin Islama ya yi maraba da shi tare da jinjina masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.