Isa ga babban shafi

Muna kan bakarmu ta haramta sanya hijabi a makarantun Faransa - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya jadda bukatar ganin lallai dalibai mata sun mutunta dokar hana sanya habaya ko hijabi a makarantun kasar, yana mai cewa duk daliban da ta yi irin wannan shiga mai nuna alaman addinin musulunci to baza ta samu damar shiga harabar makaranta ba, yayin da ake komawa azuzuwa a mako mai zuwa. 

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. via REUTERS - POOL
Talla

Ministan Ilimin Faransa, Gabriel Attal ya sanar da haramcin yayin wani taron manema labarai kwanaki shida da suka gabata ciki harda jallabiya da wasu dalibai maza ke amfani da ita, lamarin da ya haifar da cece-kuce. 

To sai dai Firanminista kasar Élisabeth Borne ta yi watsi da duk wani zarge-zargen rashin adalci kan wannan haramci, inda ta zargi masu sukar matakin da kokarin haifar da rudani a kasar. 

Sabuwar dokar dai ta sha suka a shafukan sada zumunta inda masu fafutuka ke cewa irin tufafin da ke rufe jiki bai kamata ya kasance abin nuna bangaranci na addini ba kuma bai kamata a hana dalibai shiga ajujuwa ba. 

Dokar wadda aka samar a shekarar 2004 da ke da nufin kiyaye tsarin addini a makarantun gwamnati, ta haramta sanya kallabi da musulmi ke yi amma kuma ta shafi manyan mabiya addinin Kirista, hular da Yahudawa ke sanyawa da ma rawani da mabiya addinin Sikh ke nadawa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.