Isa ga babban shafi

Gwamnan babban bankin Turkiya Hafize Gaye Erkan ta yi murabus daga mukaminta

Hafize Gaye Erkan Gwamnan babban bankin Tukiya da ta shafe kasa da shekara guda a wannan mukami ta sanar da yin murabus a jiya Juma'a a kamar yada ta wallafa a shafukan sada zumunta, sakamakon wata badakala da ta shafi 'yan uwanta.

 Hafize Gaye Erkan,Tsofuwar babban Gwamnan  bankin Turkiya
Hafize Gaye Erkan,Tsofuwar babban Gwamnan bankin Turkiya AFP - HANDOUT
Talla

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya maye gurbinta da mataimakinta,tsohon masanin tattalin arzikin Amazon Fatih Karahan, wanda aka haifa a shekarar 1982.

Fatih Karahan ya fara aikin a matsayin masanin tattalin arziki a babban bankin tarayya na New York na kasar Amurka a shekarar 2012.

Hafize Gaye Erkan,tsofuwar Gwamnan babban bankin Turkiya
Hafize Gaye Erkan,tsofuwar Gwamnan babban bankin Turkiya © AP/Business Wire

Ya koma Amazon a shekarar 2022, da kuma babban bankin Turkiya a watan yulin shekarar 2023.

Yan lokuta da sauka daga wannan mukami daga uwargida Hafize Gaye Erkan, Shugaban kasar Erdogan ya tabbatar da Fatih Karahan, a wani lokaci a can baya da kasar ta yi fama da matsalollin tattalin arziki.

Kafofin yada labaran Turkiya da dama na zargin Hafize Gaye Erkan da laifin baiwa danginta dama a babban bankin kasar, lamarin da ta musanta.

Shugaban Turkiya ,Recep Tayyep Erdogan
Shugaban Turkiya ,Recep Tayyep Erdogan © Denes Erdos / AP

Hafize Gaye Erkan, tsofuwar Gwamnan mai shekaru 44 da haihuwa, mace ta farko a wannan matsayi kuma ta yi fice saboda kwarewarta a Amurka, ta fara aiki ne a farkon watan Yuni bayan sake zaben shugaba Erdogan.

Ana zarginta da laifin barin mahaifinta ya yanke hukunci ba bisa ka'ida ba a babban bankin kasar.

A cewar masu lura da al'amuran yau da kullun, ta fuskanci fushin shugaban ne a lokacin da ta shaida wa wata jaridar kasar Turkiya a watan Disamba cewa an tilasta mata komawa zama da iyayenta, tare da 'ya'yanta da mijinta, saboda hauhawar farashin kayayyaki da wasu dalilai daban.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.