Isa ga babban shafi

Turkiyya ta kama sama da mutum 300 bisa zargin ta'addanci

Hukumomin kasar Turkiyya sun kama mutane 304 da ake zargi da alaka da kungiyar IS a wasu larduna 32, kamar yadda ministan cikin gidan kasar, Ali Yerlikaya ya tabbatarwa a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter.

Osman Baydemir, dan majalisa a jam'iyyar KPD, lokacin da ya jagoranci tawagar jam'iyyar zuwa kudu maso yammacin garin Cizre da ke kusa da lardin Idil yayin wata zanga-zangar adawa dda gwamnatin Erdogan aranar 10 ga Satumba, 2015.
Osman Baydemir, dan majalisa a jam'iyyar KPD, lokacin da ya jagoranci tawagar jam'iyyar zuwa kudu maso yammacin garin Cizre da ke kusa da lardin Idil yayin wata zanga-zangar adawa dda gwamnatin Erdogan aranar 10 ga Satumba, 2015. REUTERS/Sertac Kayar
Talla

Yawancin wadanda ake zargin an tsare su ne a manyan biranen Turkiyya uku da suka hada da Ankara, Istanbul da Izmir, kuma an gudanar da aikin binciken maboyarsu ne a lokaci guda a fadin kasar.

Faifan bidiyon da ke yawo a kafofin sada zumunta ya ya nuna yadda 'yan sanda ke shiga cikin gidaje. gine-gine da kuma cikin manyan motoci da kanana domin gudanar da bincike.

Kungiyar IS dai ta mallaki kashi daya bisa uku na Iraki da Siriya a shekarar 2014. Ko da na samu nasarar rage karfinta, amma duk da haka tana ci gaba da kai hare-hare ta’addancci.

Ta kai hare-hare da dama a fadin kasar Turkiyya, ciki har da wani gidan rawa da ke Istanbul a ranar 1 ga watan Janairun 2017, inda mutane 39 suka mutu.

Hukumomin kasar sun zafafa kai hare-hare kan mayakan IS da na Kurdawa a ‘yan makonnin nan, bayan da mayakan Kurdawa suka tayar da bam a kusa da gine-ginen gwamnati a Ankara a ranar 1 ga Oktoba.

Turkiyya na kai hare-hare a cikin gida da kuma arewacin Iraki kan kungiyar PKK wacce take daukarta a matsayin kungiyar ta'addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.