'Yan sandan Turkiya sun cafke mutane fiye da 100 bisa zarginsu da ta'addanci
Jami’an tsaron Turkiyya sun kama mutane 110 bisa zarginsu da alaka da ta'addanci, makwanni uku kacal kafin kada kuri'a a zaben ranar 14 ga watan Mayu, wanda da ake sa ran zai tsawaita wa'adin mulkin shugaba Recep Tayyip Erdogan da tsawon shekaru goma.
Wallafawa ranar:
Bayanai sun ce jami’an tsaron sun kai samame ne a sassan larduna 21, cikinsu har da yankin Diyarbakir da ke kudu maso gabashin kasar ta Turkiya, wanda kuma mafi rinjayen mazaunansa Kurdawa ne.
Sai dai kungiyar lauyoyin yankin Diyarbakir ta ce adadin mutanen da ake tsare da su zai kai 150, cikinsu kuma har da lauyoyi 20, ‘yan jarida biyar, ‘yan wasa uku da kuma dan siyasa daya.
Kafar yada labaran kasar ta TRT ta rawaito cewa, 'yan sanda sun cafke mutanen fiye da 100 ne, bisa zarginsu da tallafa wa haramtacciyar kungiyar PKK.
Kamen ya kuma shafi wasu da ake zargi da aika kudi zuwa ga kungiyar ta PKK, ta hannun wasu kananan hukumomin da ke karkashin ikon babbar jam'iyyar adawa ta Turkiya HDP.
PKK wadda Amurka da Tarayyar Turai da Turkiyan suka sanya ta cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda, ta shafe gwamman shekaru tana fafatawada sojojin gwamnati da zummar neman 'yancin cin gashin kai ga tsirarun Kurdawa.
Shugaban Turkiya Recep Tayyib Erdogan dai ya sha zargin cewa akwai alaka tsakanin jam'iyyar adawa ta HDP da PKK, zargin da jam'iyyar ta musanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu