Isa ga babban shafi

Erdogan ya ce "ba shi da alaka" da hukuncin da aka yanke wa magajin garin Istanbul

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan a yau asabar  ya bayyana  cewa "ba shi da alaka" da kamen magajin birnin Istanbul wanda ya janyo zanga-zangar 'yan adawar Turkiyya da kuma sukar kasashen duniya.

Recep Tayyip Erdogan
Recep Tayyip Erdogan © Burhan Ozbili / AP
Talla

Dubun dubatar jama'a ne suka hallara a birnin Istanbul ranar Alhamis domin marawa magajin garin birnin Imamoglu, wanda ake gani a matsayin dan takarar jam'iyyar adawa da ke iya takawa shugaban kasar birki,wanda ya lashe babban birnin Turkiyya daga jam'iyyar AKP ta shugaban Erdogan a watan Mayun 2019.

Hukuncin nasa ya kuma janyo rashin amincewar kasashen duniya da dama, inda Amurka ta ce ta damu matuka da takaici, ita kuma Jamus  ke cewa hakan ya haifar da "barna ga demokradiyya".

A watan Yuni ne Erdogan ya sanar da takararsa a zaben shugaban kasa da za a yi a shekarar 2023, amma kawancen 'yan adawa da ya kunshi jam'iyyu shida, ba su zabi dan takararsu ba.

Shugaban na Turkiyya ya ce "Ba ruwanmu da wanda zai zama dan takarar adawa." Ya yi kira ga ‘yan adawa da su yi jajircewa wajen bayyana dan takararsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.