Turkiya ta yi watsi da sakon jaje da Amurka ta aika mata
Turkiya ta yi watsi da jajen da Amurka ta yi mata game da wani harin bam da ya kashe mutane 6 a birnin Santanbul tare d jikkata wasu gommai, yayin da ake zargin mayakan Kurdawa da kaddamar da farmakin.
Wallafawa ranar:
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sha zargin Amurka da bai wa mayakan na Kurdawa makamai a yankin arewacin Syria.
Gwamnatin Turkiya ta haramta kungiyar ‘yan tawayen Kurdawa, kuma tana kallon su a matsayin ‘yan ta’adda.
A wani jawabinsa da aka watsa ta kafar talabijin, Ministan Harkokin Cikin Gidan Turkiya Suleyman Soylu ya ce, ba su karbi sakon jaje da ya fito daga ofishin jakadancin Amurka ba.
Tuni hukumomin Turkiya suka ce, sun cafke wata mata ‘yar asalin kasar Syria wadda kuma ke yi wa mayakan Kurdawa aiki bisa zargin ta da hannu wajen kai farmakin na ranar Lahadi.
Koda yake har yanzu, kungiyar Kurdawa ba ta fito karara ta dauki alhakin farmakin ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu