Isa ga babban shafi

Macron ya roki Erdogan ya daina taimakon Rasha wajen kaucewa takunkuman EU

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya roki takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da ya guji taimakawa Rasha wajen kaucewa takunkuman da kasashen yammacin Turai da Amurka suka kakabawa Rashan saboda yakin da ta kaddamar akan makwabciyarta Ukraine.

Ganawar shugaba Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa na Turkiya Recep Dayyib Erdogan.
Ganawar shugaba Emmanuel Macron na Faransa da takwaransa na Turkiya Recep Dayyib Erdogan. AP - Wolfgang Rattay
Talla

Macron ya bayyana cewa, sai Rasha taji jiki daga takunkuman da EU ke kakaba mata ne za ta hankalta wajen kawo karshen mamayar da ta ke ci gaba da yi wa Ukraine.

Bayan ganawa tsakanin Macron da Erdogan a Prague, fadar Elysee ta fitar da sanarwar cewa shugabannin biyu sun yi doguwar tattaunawa kan matakan dakile mamayar Rasha a Ukraine.

A baya bayan nan kasashen Turai da Amurka sun bayyana damuwa kan cewar Turkiyya wadda har zuwa yanzu ba ta sanyawa Moscow takunkumi kan abin da ta ke yi a Kiev ba, na bayar da mafaka ga dubunnan ‘yan kasuwar Rasha da ke neman kaucewa takunkuman kasashen yamma.

Wata Kididdiga ta nuna cewar kasuwanci tsakanin Turkiya da Rasha ya yi matukar habaka bayan da Moscow ta kaddamar da yaki kan Ukraine, lamarin da ya fusata Amurka matuka.

Amurka ta yi gargadin cewa, ko dai Turkiya ta rage yawan kasuwancin da ke tsakaninta da Rasha ko kuma ta iya fuskantar takunkuman karya tattalin arziki.

Haka zalika ko a yau juma’a sai da kungiyar EU ta sake kakaba wasu sabbin takunkumai 8 kan Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.