Isa ga babban shafi

An fara tuhumar wasu jami'an Ukraine da satar kudin makamai

A yayin da dakarun Ukraine ke fama da fafata yaki tsakaninsu da takwarorinsu na Rasha a bakin daga, a can cikin gida, sakamakon binciken da gwamnati ta gudanar, ya bankado cewar wasu jami’an hukumar kula da makaman kasar ta Ukraine sun hada baki da takwarorinsu na ma’aikatar tsaro, wajen karkatar da kusan dala miliyan 40, da aka ware domin sayen makamai.

Wasu sojojin Ukraine yayin kai hari kan sojojin Rasha a kusa da garin Avdiivka da ke yankin Donetsk. 26 ga Disamba, 2022.
Wasu sojojin Ukraine yayin kai hari kan sojojin Rasha a kusa da garin Avdiivka da ke yankin Donetsk. 26 ga Disamba, 2022. AP - Libkos
Talla

Masu gabatar da kara sun ce zuwa yanzu mutane 5 aka gurfanar gaban kotu kan almundahanar, yayin da ake tsare da wani guda da aka cafke shi a lokacin da yake kokarin tsallaka iyaka don ficewa daga kasar ta Ukraine.

Idan har aka kama jami’an da laifin da ake tuhumarsu da aikatawa, suna iya fuskantar hukuncin daurin shekaru akalla 12 a gidan Yari.

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky.
Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky. AP - Virginia Mayo

Wannan dambarwa na zuwa ne yayin da shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy yayi gargadin cewa raguwar tallafin da suke samu daga Amurka kan yakin da suke yi da Rasha ba fa zai haifar da mai ido ba.

Gargadin na Zelenskyy dai ya biyo bayan turjiyar da shugaba Joe Biden ke fuskanta daga ‘yan majalisar dokoki na jam’iyyar Republican, masu adawa da taimakon biliyoyin dalar da Amurka ke bai wa Ukraine.

Wannan kalubale ne ya sanya shugaba Zelenskyy yin kira ga Jamus da ta yi amfani da tasirinta na tattalin arziki, wajen neman hadin kan sauran kasashen kungiyar EU kan bukatar cike gibin da Amurka ta bari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.