Isa ga babban shafi

Rayukan mutane 74 sun salwanta bayan harbo jirgin yakin Rasha a Belgorod

Rasha ta zargi Ukraine da harbo jirgin saman sojanta da gangan, yayin da yake kan hanyar kai sojojin kasar ta Ukraine din guda 65 da ta kama, zuwa inda aka shirya kasashen biyu za su yi musayar fursunoni.

Yadda hayaki ya turnuke a wani yankin birnin Belgrod na Rasha mai iyaka da kasar Ukraine.
Yadda hayaki ya turnuke a wani yankin birnin Belgrod na Rasha mai iyaka da kasar Ukraine. via REUTERS - BELPRESSA
Talla

Tuni dai aka tabbatar da mutuwar dukkanin mutane 74 da ke cikin jirgin sojin na Rasha.

Jirgin yakin da aka kakkabo a gaf da birnin Belgrod da ke kusa da iyakar Rasha da Ukraine ya kunshi ma'aikata 6, da masu gadi uku, sai kuma sojojin Ukraine 65, da aka kama a matsayin fursuna.

Cikin wata hira da manema labarai jim kadan bayan aukuwar lamarin, Andrei Kartapolov, dan majalisar dokokin Rasha kuma Janar mai ritaya, ya ce da gangan aka kakkabo jirgin yakin nasu don yin zagon kasa ga musayar fursunonin da ake shirin aiwatarwa.

Kartapolov, wanda har yanzu ke da alaka ta kusa da ma'aikatar tsaron Rasha, ya ce an harbo jirgin ne da makamai masu linzami guda uku wadanda suka kasance ko dai kirar Amurka ko kuma na Jamus.

Yankin Belgorod na Rasha da ke kusa da iyakar Ukraine na fuskantar hare-hare akai-akai daga sojojin kasar a 'yan watannin nan, ciki har da harin makami mai linzamin da ya halaka mutane 25 a karshen watan Disambar da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.