Isa ga babban shafi

Jiragen saman Amurka sama da dubu biyu sun tsaida aiki saboda matsalar sauyin yanayi

Kamfanonin jiragen sama a Amurka sun soke harkokin sufuri na jiragen kasar sama da 2000, biyo bayan gagarumar iskar bazara da ta yi sanadiyar katsewar wutan lantarki ta kuma shafi kasuwanni da dama a cikin jahohi 12 dake fadin kasar, abinda ya sa ake ganin za a yi sanyi mai tsananin ranar asabar da lahadi. 

wani jirgin saman Kasar Amurka
wani jirgin saman Kasar Amurka JOE RAEDLE / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP
Talla

Akalla jirage dubu 2,058 aka dakatar da aikinsu a jiya juma'a, yayin da aka jinkirta lokacin tashi na wasu jiragen dubu 5,846 kamar yadda Hukumar dake kula da harkokin sufurin jiragen saman kasar ta sanar. 

Kamfanin jiragen saman Amurka dake yankin kudu maso yammaci LUV.N ke kan gaba a cikin jerin jiragen da aka dakatar daga tashi, da adadin jiragenta 401, sannan jiragen saman Skywest da adadi 358.

Kamfanin Delta dake da jiragen sama a sassan kasar, ya ce akwai yiwuwar su fuskanci kalubale a ranar asabar da lahadi saboda yanayi na saukar dusar kankara da aka soma, yayin da kamfanin na LUV. N ke cewa matsalar za ta shafi wasu daga cikin jiragensa a biranen Chicago da Detroit da kuma Omaha. 

Tun a ranar alhamis da ta gabata ne hukumar dake kula da harkokin sufurin jiragen saman Amurka ta gargadi batun matsalolin da sayin yanayin ke tafe da su a wannan lokaci da suka hada da saukar dusar kankara da yadda isakar bazara ke haifar da tsaiko wajen tashi da saukar jiragen saman kasar da dama. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.