Isa ga babban shafi

Girgizar kasa ta kashe sama da mutane 100 a arewa maso yammacin China

A kalla mutane 116 ne suka mutu sakamakon girgizar kasar da ta ruguje gidaje a arewa maso yammacin kasar China, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito da safiyar Talatan nan, yayin da jami’an ceto suka dukufa wajen tona baraguzan gine-gine cikin wani yanayi mai sanyin gaske.

Masu aikin ceto na binciken baraguzan gidan da girgizar kasar ta lalata a Kangdiao, lardin Gansu, 19 ga Disamba, 2023.
Masu aikin ceto na binciken baraguzan gidan da girgizar kasar ta lalata a Kangdiao, lardin Gansu, 19 ga Disamba, 2023. AP
Talla

Jami’ai a lardin Gansu da lamarin yafi muni sun ce kimanin mutane 105 ne suka mutu sannan kusan 400 suka jikkata, sakamakon girgizar kasa mai karfin gaske da ta afku da tsakar dare.

Gidan talabijin na kasar CCTV, ya ruwaito cewar, a can birnin Haidong na lardin Qinghai mai makwabtaka kuwa girgizar kasa ta kashe mutane 11 tare da jikkata wasu 100.

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya bayyana cewa, girgizar kasar mai karfin maki 5.9 ta yi barna sosai, da suka hada da rugujewar gidaje, tare da warwatsa bin titi domin neman tsira.

An fara aikin ceto da sanyin safiyar Talata, inda shugaban kasar Xi Jinping ya yi kira da akara azama a aikin ceto da kuma tabbatar da tsaron wadanda suka tsira da kuma dukiyoyinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.