Girgizar kasa a gabashin China ta ruguza gidaje tare da jikkata akalla 21
Wata girgizar kasa a gabashin China ta rusa gidaje tare da raunata akalla mutane 21, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana, amma ba a samu asarar rai ba.
Wallafawa ranar:
Girgizar kasar mai karfin maki 5.5 ta afku a kusa da birnin Dezhou mai tazarar kilomita 300 kudu da birnin Beijing, babban birnin kasar, da misalign karfe 2:30 na safe.
Hukumomin kasar sun ce, an ji alamar motsin kasa a wasu sassan birnin Beijing, amma ba a samu barna a babban birnin kasar ba.
Yankin Dezhou da kewayen birnin na da kusan mutane miliyan 5.6, a cewar hukumar kula da yawan jama'a ta kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu