Isa ga babban shafi

Ministan kula da albarkatun Azerbaijan zai jagoranci taron sauyin yanayi na COP29

Gwamnatin Azerbaijan ta sanar cewa ministan kula albarkatun kasar Mukhtar Babayev ne zai jagoranci taron sauyin yanayi mai zuwa COP29, wanda zai gudana cikin watan Nuwanba mai zuwa a babban birnin kasar Baku. 

Mukhtar Babayev da zai jagoranci taron sauyin yanayi na COP29 a Azerbaijan.
Mukhtar Babayev da zai jagoranci taron sauyin yanayi na COP29 a Azerbaijan. AP - Rafiq Maqbool
Talla

Gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ce ta yi sanarwar a shafinta na X da aka fi sani da tweeter, bayan kawo karshen taron COP28 a kasar. 

Kafin zama minista, Babayev ya yi aiki karkashin kamfanin man kasar Socar na tsawon shekaru 24, kazalika ya rike mukamin mataimakin shugaban kamfanin. 

Zaben Babayev, cigaba ne a zaben masu karfin alaka da Kamfanin mai da iskar gas dake jagorancin taron sauyin yanayi karkashin Majalisar dinkin duniya.

Azerbaijan dai daya ce daga cikin kasashe dake kan gaba wajen fitar da iskar gas, kuma a yanzu haka ta na da cubic mita triliyan 2.5 na iskar gas a rumbunta. 

A cikin shekarar da ta gabata aka gudanar taron sauyin yanayin na COP28 a birnin Dubai,  wanda shugaban babban kamfanin man Abu Dahbi, Sultan Al Jaber ya jagoranta. 

A cikin watan nuwamban shekarar bara Kafofin yada labarai suka bayyana cewa UAE na shirin tattauna batun kulla wasu yarjeniyoyi na kasuwanci gabanin taro mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.