Isa ga babban shafi

Amurka ta sake kaddamar da sabon farmaki a Yemen

Amurka ta sake kaddamar da wani sabon farmaki a Yemen biyo bayan shan alwashi da Joe Biden ya yi na kare jiragen ruwan dakon kaya da ke ratsa tekun Bahar Maliya. 

Jirgi a kan tekun Bahar Maliya
Wani jirgin ruwan a tekun bahar maliya AP - LPhot Belinda Alker
Talla

Harin na zuwa ne kwana guda bayan makamancinsa da Amurka da takwararta Birtaniya suka kaddamar a kan jiragen yakin dakarun Houthi dake kan tekun, lamarin da ke kara jefa fargabar cigaba da yaduwar rikicin Isra’ila a gabas ta tsakiya.

Wannan na zuwa ne bayan hare-hare kan jiragen kasashen da mayakan na Houthi suka kai don jadadda barazanar su ta hana kaya shiga Isra’ila ta tekun, matukar bata dakatar da ruwan wutar da take yi a Gaza ba.

Ganau sun shaida wa manema labarai cewa kasashen sun yi amfani da bama-bamai wajen kai wa jiragen mayakan Houthi hari a kan gabar tekun Maliya ta Hodeidah da kuma gab da sansanin soji na Hajja.

Tun a jiya juma’a ne dubban mutane suka gudanar da zanga-zanga a birane da dama na kasar Yemen, don nuna bacin rai dangane da hare-haren da jiragen yakin Birtaniya da Amurka suka kai wa cibiyoyin mayakan kungiyar Houthi da ke rike da madafan iko a kasar. 

Tuni dai Iran ta yi Allah wadai da wannan hari tana mai kwatanta shi da tsokanar fadan da zai mamaye yankin gabas ta tsakiyta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.