Isa ga babban shafi

Putin ya yi watsi da ikirarin Biden na cewa Rasha na shirin kai wa NATO hari

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi watsi da ikirarin Amurka na cewa Moscow na iya kai hari kan wata kasa mamba a kawance tsaro ta NATO idan ta yi nasara a kan Ukraine, yana mai bayyana ikirarin a matsayin “shirmen banza" domin yin haka zai ci karo da muradun kasarsa.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin © AP - Mikhail Klimentyev摄影
Talla

Mista Putin ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na kasar Rasha wannan Lahadi, makonni bayan da shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yi gargadin cewa idan Putin ya samu nasara a Ukraine, mai yiwuwa ya samu kwarin guiwa wajen kai hari kan wata kasa dake cikin kawancen NATO, lamarin da ka iya haifar da yakin duniya na uku.

"Wannan shirme ne - kuma ina tsammanin Shugaba Biden ya fahimci hakan, Rasha ba ta da wani dalili ko sha'awar fadada yakinta ga kasashen NATO saboda bai da wani tasiri”

Putin ya kara da cewa watakila Biden yana kokarin tayar da irin wannan fargaba don tabbatar da manufofinsa masu cike da kurakurai a yankin.

Dangantakar Amurka da Rasha ta tabarbare a baya-bayan nan tun bayan da Moscow ta mamaye makwabciyarta Ukraine a watan Fabrairun 2022.

Kuma cikin yakin na watanni 22, Amurka ta ba wa Ukraine tallafin dala biliyan 111 na makamai, bayaga sauran taimako.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.