Isa ga babban shafi

Putin na Rasha zai sake tsayawa takara bayan shekaru 20 kan karaga

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana anniyarsa ta tsayawa takara a zaben shekarar 2024, abin da  zai ba shi damar ci gaba  da mulkin kasar har zuwa cikin shekarun 2030, bayan da ya  riga ya shafe shekaru sama da 20  yana jagorancin kasar. 

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin AP - Mikhail Klimentyev
Talla

Putin mai shekaru 71 ya karbi  ragamar mulkin Rasha ne tun da aka shiga wannan karni na 21, inda bayan haka ya lashe zabe har sau 4, ya kuma rike mukamin firaminista  na dan gajeren lokaci. 

Shugaban na Rasha ba zai fuskanci wani kalubale mai karfi ba a kokarinsa na neman wa’adi na biyar a matsayin shugaban kasar, kuma biyo bayan wata  kwaskwarimar da aka wa kundin tsarin mulkin kasar a shekarar  2020, wadda ta janyo cece-kuce, Putin na iya  ci gaba da  mulkin wannan kasa har zuwa akalla shekarar 2036. 

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun yi zargin cewa an tafka magudi a zabukan da aka gudanar a kasar a baya, kuma akwai yiwuwar a haramta duk wani aiki na sanya  ido a zabe mai zuwa. 

A watan Nuwamba, Putin ya tsaurara dokokin da suka shafi daukar rahotanni a kan zaben 2024, yana mai haramta wa wasu kafafen yada labarai masu cin gashin kansu damar zuwa rumfunan zabe. 

Abokin hamayyar Putin na gidi dai shi ne Alexei Navalny, wanda  yanzu haka yake zaman gidan yari na shekaru 19 sakamakon laifukan da  magoya bayansa suka bayyana a matsayin kage.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.