Isa ga babban shafi

Putin ya yi alkawarin taimaka wa kasashen Afirka da kayan abinci

Shugabannin kasashen Afirka sun halarci taro da takwaransu na Rasha Vladimir Putin, wanda ya daukar musu alkuwura kan sama wa kasashensu kayan abinci dangin hatsi don cike gibin da suke fuskanta, tare da yi musu karin bayani akan makomar ayyukan sojojin haya na kamfanin Wagner a nahiyar Afirka.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin AFP - PAVEL BEDNYAKOV
Talla

Taron ya gudana ne a birnin St Petersburg kwanaki 10 bayan da Putin ya fice daga yarjejeniyar bai wa Ukraine damar fitar da hatsi da jigilarsu zuwa kasashe marsa karfi cikinsu har da na Afirka, daga tashar jiragen ruwa a yankin kudancinta.

Tuni dai farashin Alkama ya karu da kusan kashi 20 cikin 100, tun lokacin da Rasha ta kawo karshen yarjejeniyar fitar da kayan abinci dangin hatsi daga Ukraine a ranar 17 ga Yuli.

Yayin fayyace dalilin daukar matakin, shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce Amurka da kawayenta na Turai tare wasu kamfanoni da ke karkashinsu ne ke amfana da yarjejeniyar jigilar hatsin na Ukraine zuwa sassan duniya, abinda ya sanya kasa da kashi 3 ne kawai na adadin abincin ya isa ga kasashe marasa karfi.

Putin ya kuma zargi kasashen na Turai da yin watsi da babbar munufar yarjejeniyar da aka kulla da zummar rage hauhawar farashin kayan abincin a sassan duniya.

Shugaban na Rasha ya ce kasarsa na sa ran samun nasarar girbin amfanin gona mai yawan gaske a shekarar bana, kuma a shirye take ta cike gibin da kasashen Afirka ke fuskanta ta hanyar samar da hatsi a kasuwanninsu, yayin da kuma za ta raba wani kaso na kayayyakin abinci a matsayin tallafi kyauta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.