Isa ga babban shafi

Denmark za ta bijiro da dokar haramci ga kona Kur'ani da sauran littafan addini

Gwamnatin Denmark ta mika wa majalisar dokokin kasar bukatar amincewa da dokar haramta kona al’qura’ni mai girma da sauran litattafan addini a gaban ofishin jakadancin kasashe. 

A kwanan baya ne wasu suka kona Kur'ani a kasar Denmark, lamarin da ya janyo martani  daga al'ummar zazzafan Musulmin duiniya.
A kwanan baya ne wasu suka kona Kur'ani a kasar Denmark, lamarin da ya janyo martani daga al'ummar zazzafan Musulmin duiniya. Fuente: Wikipedia.
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Lars Lokke Rasmussen ne bayyana hakan ta cikin wata tattaunawa da kafar talabijin din kasar wato DR, yana mai cewa lokaci yayi da kasar za ta haramta kona litatttafan addini da nufin tunzura mabiya addinin. 

Ministan, wanda ke bada misali da abin da ya faru a baya-bayan nan, ya ce kona al-quranin da aka rika yi a kasar kawai don ya faru a kasar Sweden ya janyo mata asara da kuma zubewar kima da lalata alakar diplomsaiyya tsakaninta da manyan kasashen Musulmi da ta ke hulda da su, yana mai cewa Prime ministan kasar Matte Frederisken tuni ya mika bukatar samar da wannan doka, abin da ya rage yanzu kawai shine sahalewar ‘yan majalisa. 

Tuni dai kasashe da dama suka dauki matakin yanke alakar diplomasiyya da Denmark da kuma Sweden saboda wannan lamari na kona al’qur’ani da ya zama tamkar wata sabuwar al’ada. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.