Isa ga babban shafi
Jamus-Denmark

Jamus na tuhumar Denmark kan zargin leken asirin Amurka

Jamus ta bukaci cikakken bayani daga kasar Denmark a game da zargin da ake yi mata na hada kai da Amurka wajen yi wa wasu shugabannin kasashen Turai leken asiri, ciki kuwa har da shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel.

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel
Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel John MACDOUGALL POOL/AFP/File
Talla

Tun da farko, wasu daga cikin kasashen Turai, sun zargi Denmark da taimaka wa Amurka wajen yin leken asiri ga manyan ‘yan siyasar yankin.

A cewar kasashen da suka yi zargin, Hukumar Tsaron Sirri ta Denmark ta hada kai da Hukumar Tsaron Sirri ta Amurka wajen ba ta bayanan da suka shafi manyan ‘yan siyasar Turai ba bisa ka’ida ba.

Cikin kasashen da suka yi wannan zargi akwai Jamus da Faransa da Sweden da kuma Norway.

Da yake jawabi shugaban kasar Jamus Frank- Walter Steinmeir ya ce, Jamus za ta kara fadada bincike kan wannan zargi da kuma duba yiwuwar daukar matakin da ya dace.

Baya ga Jamus din ana sa ran wasu kasashen su ma za su dauki matakin neman cikakken bayani daga Jamus  la’akari da yadda suka sha alwashin daukar mataki yayin da wasu suka ce za su mayar da martani cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.