Denmark za ta takaita kwararar ‘Yan gudun hijira
Majalisar Denmark ta amince da sabbin dokokin rage kwararar baki ‘Yan gudun hijira da ‘yan ci rani, matakin da ya janyo suka ciki da wajen kasar.
Wallafawa ranar:
Sabbin dokokin ‘Yan Majalisa suka amince a yau Talata sun kunshi takaita ba bakin damar shigar da ‘yan uwansu bayan sun samu damar izinin zama a kasar.
Sannan za a kwace wasu kadarorinsu da suka mallaka a cikin kasar ta Denmark.
Matakin dai ya janyo suka a ciki da wajen kasar kan tsauraran matakan da Denmark ta dauka.
Gwamnatin kasar ta ce ya zama wajibi ta dauki matakin domin dakile kwararar baki yan gudun hijira.
Tuni dai Denmark da Sweden suka tsaurara matakai a kan iyakokinsu domin rage kwararar ‘yan gudun hijira mafi yawancinsu ‘yan kasashen Syria da Iraqi da Afghanistan da ke kauracewa yaki.
‘Yan rajin kare hakkin bil’adama dai sun yi kakkausar suka kan matakan da Denmark ke son dauka wanda suka ce ya sabawa dokin kasa da kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu