Faransa za ta fara ruguza runfunan ‘Yan ci-rani a Kurmin Calais
Hukumomin Faransa za su fara ruguza sansanin da ‘Yan ci rani suka kafa a yankin Calais da nufin tsallakawa zuwa Birtaniya, yayin da kasar za ta fara mayar da su cikin wani sansani da aka inganta don kare lafiyarsu da kuma samar da tsaro.
Wallafawa ranar:
Gwamnatin kasar tace tana sa ran kwashe baki ‘Yan ci-ranin da ‘Yan gudun hijira tsakanin 500 zuwa 700 don mayar da su sabbin wuraren da ke da abubuwan more rayuwa da suka hada da wutar lantarki da na’urar dumama daki da kuma ta kula da jirirai.
Sai dai bakin na fargabar zuwa sansanin da aka samar saboda matakan tsaro musamman tantance masu shiga da fita.
Faransa da Birtaniya dai sun kashe makudan kudade domin inganta tsaro a kan iyakokinsu musamman yankin Calais inda dubban ‘Yan ci rani ke kokarin tsallakawa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu