Isa ga babban shafi
Turkiya

Turkiya ta amince da bukatun Turai kan ‘Yan gudun hijira

Kasar Turkiya ta amince ta dauki matakai a kan iyakokinta domin rage kwararar ‘Yan gudun hijira zuwa kasashen Turai a wata yarjejeniya da kasar ta kulla da kungiyar kasashen Turai a Brussels.

Firaministan Turkiya Ahmet Davutoglu tare da Shugaban kungiyar Turai Jean-Claude Juncker a taron Brussels
Firaministan Turkiya Ahmet Davutoglu tare da Shugaban kungiyar Turai Jean-Claude Juncker a taron Brussels REUTERS/Yves Herman
Talla

Karkashin yarjejeniyar Turkiya za ta karbi tallafin kudi yuroo biliyan uku a matsayin agaji, yayin da ita kuma a bangarenta zata dauki matakan hana kwararar baki ‘yan gudun hijirar Syria zuwa Nahiyar Turai.

Shugaban kungiyar kasashen Turai Donald Tusk ya ce aiwatar da yarjejeniyar hana ‘Yan gudun hijira shiga Turai daga kasar, mataki ne da zai bai wa Turkiya damar komawa tattaunawar samun wakilci a kungiyar.

Firaministan Kasar Ahmet Davutoglu ya bayyana yarjejeniyar a matsayin mai cike da tarihi inda yayi alkawarin cewar Turkiya zata cika alkawarin da ta dauka.

Kimanin Baki 850,000 suka tsallaka zuwa Turai a bana kuma Turkiya ta kasance mashigin ‘Yan gudun hijirar na Syria zuwa kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.