Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta bukaci a sa ido ga ‘Yan Syria

Kasar Faransa ta bukaci kungiyar kasashen Turai da ta dada sa ido ga fasfo na bugi da wasu ke amfani da shi a matsayin na kasar Syria, musamman a kasashen Girka da Italia bayan kazamin harin da aka kai birnin Paris.

Ministan cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve
Ministan cikin gidan Faransa Bernard Cazeneuve AFP PHOTO / STEPHANE DE SAKUTIN
Talla

Ministan cikin gida Bernard Cazeneuve yac e binciken kwa-kwaf kan fasfo da baki ‘Yan gudun hijira da ‘yan ci-rani ke gabatar wa a iyakokin Turai na da matukar tasiri domin kare al’ummar nahiyar.

Minsitan ya ce an sace fasfo din jama’a da dama a Yankunan da mayakan IS suka mamaye kuma wasu na amfani da su domin shiga kasashen Nahiyar Turai.

Akwai fasfo din Syria da aka tsinta kusa da gawar daya daga cikin maharan da suka kai jerin hare hare a Paris a ranar 13 ga watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.