Isa ga babban shafi

Gwamnatin Italiya ta ware sama da Yuro biliyan 2 ga wadanda ambaliya ta shafa

Firaministar Italiya Giorgia Meloni ta sanar da ware sama da Yuro biliyan biyu ga yankin Arewa maso gabashin Emilia Romagna da ambaliyar ruwa ya lalata da kuma sanadin mutuwar mutum 14.

Wakilan fadar gwamnatin Italiya kenan da suka kai ziyara wani yanki da ambaliyar ruwa ta shafa.
Wakilan fadar gwamnatin Italiya kenan da suka kai ziyara wani yanki da ambaliyar ruwa ta shafa. AFP - HANDOUT
Talla

Majalisar ministocin Meloni ta rattaba hannu kan wata doka wacce ta tanadi ware sama da Euro biliyan biyu ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa, daga manoma zuwa makarantu, ayyukan kula da lafiya da kuma masana'antar yawon bude ido.

Wasu yankunan Emilia Romagna har yanzu suna karkashin ruwa bayan ruwan sama na tsawon watanni shida a cikin sa'o'i 36 da ya wuce, kuma ya zuwa ranar litinin, mutane 23,000 sun fice daga gidajensu.

An sake bude makarantu a Ravenna a ranar Talata, kodayake manyan makarantun da ke kusa da Forli sun kasance a rufe har zuwa ranarLaraba saboda katsewar hanyoyin sadarwa.

Yankin dai an yi kiyasin cewa barnar da ruwa ya yi ya lakume dukiya ta sama da Yuro miliyan 620 kama daga ababen more rayuwa da suka hada da tituna da hanyoyin jiragen kasa.

Tafkunan yankin sun tumbatsa da ruwa saboda mamakon ruwan sama, abin da ya haifar da ambaliyar har zuwa makwabtan yankin, lamarin da ya lalata gonaki da kuma masana’antu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.