Isa ga babban shafi

An ayyana dokar ta baci a Italiya saboda zaftarewar kasa a wani tsibiri

Italiya ta ayyana dokar ta baci a tsibirin Ischia da ke kudancin kasar bayan zaftarewar kasa ta hallaka mutane akalla bakwai tare da bacewar wasu da dama.

Masu aikin ceto na tattauna yadda za su ciro motar da ta makale a tsibirin Ischia, kusa da Naples, a yammacin Italiya.
Masu aikin ceto na tattauna yadda za su ciro motar da ta makale a tsibirin Ischia, kusa da Naples, a yammacin Italiya. AP - Salvatore Laporta
Talla

Lamarin ya auku ne a wani karamin garin Casamicciola Terme a safiyar ranar Asabar, inda ya lalata gidaje tare da awon gaba da motoci zuwa teku.

Kafofin yada labaran yankin sun ce tarin laka da baraguzai sun zaftaro a kan karamin garin da safiyar Asabar,  lamarin da ya rufe akalla gida guda, tare da share dimbim motoci zuwa cikin teku.

An saki kashi na farko na kudi Yuro miliyan 2 da aka ware a matsayin kudin rage radadi a taron majalisar zartaswa da aka gudanar.

Sama da masu aikin ceto 200 ne ke ci gaba da lalubo mutanen da suka bace, a yayin da daruruwar ‘yan aikin sa kai , wadanda ke ciki laka har gwiwa suna ta aikin sharar tituna.

Aikin ceton na samun cikas sakamakon ruwan sama da iska mai karfi da ake ta yi, wanda ya janyo tsaiko ga aikin igilar kayan agaji da ma’aikata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.