Isa ga babban shafi

Mutane 13 sun bace sakamakon zabtarewar kasa da ruwan sama a Italiya

Mutane 13 ne suka bace a safiyar ranar Asabar bayan zabtarewar kasa sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a tsibirin Ischia na Italiya da ke kusa da Naples,kamar yada kamfanonin dillancin labaran Italiya ANSA da AGI suka ruwaito.

Al'amarin ambaliya a wasu kasashen Duniya
Al'amarin ambaliya a wasu kasashen Duniya REUTERS - ALY SONG
Talla

Zabtarewar kasa ta afku ne a garin Casamicciola Terme da ke arewacin tsibirin, kuma ta lakume wani gida tare da jan motoci da dama a cikin tekun, in ji hukumar kashe gobara, ta kara da cewa suna neman wadanda suka bata.

A cewar hukumomin, mutane goma sha uku ne suka bace a karshen safiya, yayin da zabtarewar ta faru da sanyin safiyar ranar Asabar.

Wata mota da ta kutsa cikin tekun akwai mutane biyu a cikinta amma an ceto su, kamar yadda ma'aikatan kashe gobara suka ce, hukumomin yankin sun yi kira ga mazauna tsibirin da su kasance a gida, tare da kawo nasu agaji a cikin ayyukan ceto.

Casamicciola Terme, wurin shakatawa da mazauna 8,000 a cikin hunturu, ya fuskanci girgizar kasa a cikin 2017 wanda ya kashe mutane biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.