Isa ga babban shafi

Italiya ta tsare tarin 'yan Najeriya a gidan yari ba tare da yi musu shari'a ba

Bakin haure ‘yan asalin Najeriya ne suke a garkame a gidajen yarin Italiya ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu don yanke musu hukunci ba.

Wani gidan yari a Turai.
Wani gidan yari a Turai. AP - Jay Reeves
Talla

Wani lauya mai fafutukar kare hakkin dan adam a Najeriya, Lucky Aghedo ne ya yi nuni da haka, inda ya ce baya ga wadanda suke a kulle, akwai wadanda aka yanke wa hukuncin zama gidan wakafi na tsawon lokaci.

Wata jaridar kasar Italiya, Gazzetta di Reggio da aka wallafa a cikin watan Afrilun wannan shekarar ta ruwaito cewa ‘yan Najeriyan 36, wadanda aka kama sakamakon zargin aikata laifuka dabam dabam ne suke a tsare a gidan yarin kasar ba tare da an yi musu shari’a ba.

Jaridar ta ce laifukan da ake zargin bakin hauren da aikatawa sun hada da satar kudi ta katin banki, sai kuma laifin shiga cikin harkar tsagerancin ‘Mafia’ da ya yi kamari a Italiya.

Lauya mai fafutukar ya bayyana damuwa  agame da halin da bakin hauren, wadanda suka hada da ‘yan wasu kasashen Afrika ke ciki, duba da cewa ba sa fahimtar yaren kasar, kumna ba su da damar daukar lauyar da zai kare su.

Lauyan ya ce tsare wadanna mutane na tsawon lokaci ba tare da an gurfanar da su a gaban kotu ba yayikaran tsaye ga dokar kare hakkin dan adam,yana mai kira ga hukumar kare hakki na Tarayyar Turai da ta duba lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.