Isa ga babban shafi

Adadin wadanda suka mutu sakamakon zaftarewar kasa a Italiya ya kai 12

Masu aikin ceto sun gano gawar mutum na karshe, bayan da laka ta danne gine-gine da mutane a tsibirin Ischia na kasar Italiya a watan jiya, wanda hakan ya tabbatar da cewa mutane 12 ne suka mutu sakamakon ibtila’in.

Masu aikin ceto kenan da suke kokarin kwaso mutanen da gini ya ruftawa yayin wata girgizar kasa Indonesia
Masu aikin ceto kenan da suke kokarin kwaso mutanen da gini ya ruftawa yayin wata girgizar kasa Indonesia AP - Rangga Firmansyah
Talla

Baraguzan gini dauke da laka sun mamaye kauyen Casamicciola Terme, ranar 26 ga watan Nuwamba, bayan mamakon ruwan sama, abin da ya haifar da lalacewar gidaje, da kuma kora motoci zuwa kogi.

Hukumar kashe gobara ta wallafa a shafinta na twitter cewa an gano gawa ta karshe da ake nema tsawon kwanaki.

Kafofin yada labaran kasar sun ruwaito cewa, masu aikin ceto sun gano gawar wata mace mai shekaru 31, a karkashin baraguzan gine-gine.

Masana ilimin kasa sun yi gargadin cewa za a iya fuskantar yanayi mai cike da hatsari da ka iya haifar da zaftarewar kasa a wasu yankuna na tsibirin, wanda ke da kusanci da Capri da masu yawon bude idanu ke yawan kai ziyara wurin.

Sama da mutane 1,000 hukumomi suka kwashe a wuraren da ke cike da barazanar fuskantar mamakon ruwan saman ranar Juma’a

Da dama daga cikin mutanen da aka kwashe suna zaune a otal-otal, inda suke dakon lokacin da gwamnati za ta mayar da su gidajensu.

Masana sun ce bala'in na watan Nuwamba ya faru ne sakamakon mummunan sauyin yanayin da kuma sare dazuzzukan da aka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.