Kotun Faransa ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 3 kan Nicolas Sarkosy
Kotun daukaka kara a Faransa ta zartas da hukuncin daurin shekaru 3 kan tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy kan laifin rashawa da amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba lokacin ya na matsayin shugaban kasar.
Wallafawa ranar:
Hukuncin na yau laraba ya nuna cewa Sarkozy zai yi zaman daurin talala na shekara 1 a cikin gidansa sai kuma haramcin rike duk wani nau’in mukami a gwamnatance har na tsawon shekaru 3.
Yayin zaman na shekara guda kotun ta yi umarnin daura mishi wani abin hannu mai nadar bayanai da zai tabbatar da kasancewar shi a cikin gidan ba tare da karya dokar tsarewar ba.
Bayan hukuncin na yau, hakan na mayar da Sarkozy matsayin tsohon shugaba na farko da zai yi yari a tarihin Faransa.
Tsohon shugaban mai shekaru 68 kotu ta same shi da laifin karbar rashawa a lokacin mulkinsa baya taurin game da tuhume-tuhumen da ake masa na amfani da ofishinsa ba bisa ka’ida ba.
Sarkozy da ya mulki Faransa daga shekarar 2007 zuwa 2012 ya rika fuskantar tuhume-tuhumen aikata ba dai dai ba a mabanbantan shari’a tun bayan barinsa ofishi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu