Isa ga babban shafi

Gwamnatin Congo ta ce ziyarar Sarkozy a kasar ba don tattaunawa ba ne

Gwamnatin Congo ta ce, ziyarar da tsohon shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy, ya kai Kinshasa babban birnin kasar, ba wai domin shiga tsakanin rikicin da ke wakana tsakanin ta da kasar Rwanda ya je ba.

Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy kenan daga dama, tare da tsohon ministan cikin gida na kasar, Claude Gueant daga hagu. An dauki hoton ranar 15 ga watan disamban 2011.
Tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy kenan daga dama, tare da tsohon ministan cikin gida na kasar, Claude Gueant daga hagu. An dauki hoton ranar 15 ga watan disamban 2011. AP - Michel Euler
Talla

Wata majiya ta ce, tsohon shugaban ya gana da shugaban Congo, Felix Tshisekedi, kan rashin jutuwar da ke wakana tsakanin gwamnatin Kinshasa da kuma Kigali.

Tina Salama, wadda ita ce kakakin gwamnatin kasar ta ce ziyarar tsohon shugaban bata da nasaba da ‘yan tawayen da suka mamaye gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

“Ziyarar da tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy ya kai Kinshasa, ba bisa gayyatar shugaban kasar Felix Tshisekedi ne ya yi ba, ziyarar ce ta kashin kan sa domin yana da wasu abubuwa da zai yi a nan,” in ji Salama.

Ta ce, an yi masa maraba a matsayinsa na tsohon shugaban kasar Faransa, said ai gwamnati bata nemi kowa ya zama mai shiga tsakani a rikicin ta da Ruwanda ba.

“Al’amuranmu da Ruwanda sananne ne, muna bukatar shugaban kasar Ruwanda ya kawar da ‘yan ta’addan da ke cikin kasar mu, da kuma daina yake-yaken da suke yi a gabashin kasarmu, in ji ta.

A ranar Laraba ne, tsohon shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy ya isa kasar, inda ya gana da hukumomin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo a Kinshasa, babban birnin kasar.

Sai dai babu wani karin haske daga bangarorin biyu kan ko Mista Sarkozy ya shirya wata tattaunawa.

An dai san Sarkozy yana kokari wajen tuntubar gwamnatocin Kinshasa da Kigali, kuma makusanci ne ga shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda shima ya kai ziyara Kinshasa kwanan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.