Isa ga babban shafi

Shugaba Macron ya ki bayyana matsayar Faransa dangane da rikicin DRCongo da Rwanda

A ziyarar da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kai birnin Kinshasa, dangane da rikicin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Emmanuel Macron, bai fito fili ya yi Allah wadai da kasar Rwanda ya yi jawabin sa a jiya Asabar ba, kamar yadda al’umar kasar ta Congo suka bukaci ya yi, amma ya yi gargadin zuwa shugabanin kasashen biyu. 

Daya daga cikin yankunan dake fama da rashin tsaro a DRCongo
Daya daga cikin yankunan dake fama da rashin tsaro a DRCongo Racove, Radio communautaire de la Vérité
Talla

DRCongo ta zargi Rwanda da goyon bayan 'yan tawayen M23, wanda tun shekara ta 2022 ta kwace yankuna da dama a lardin Kivu ta Arewa, yankin mai arzikin ma'adinai. Kwararru na Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar da wannan kutse kuma wasu shugabannin kasashen Yamma sun yi Allah wadai da shi, ko da yake Rwanda ta musanta hakan. 

Ma'aikatar haarkokin wajen Faransa ma ta yi Allah wadai da wannan tallafin, amma Kinshasa na fatan daukar kwararan matakai kan Kigali daga Paris. 

Emmanuel Macron bai sanar da wani takunkumi ba, amma ya yi kira ga kowa da kowa da ya "dauki alhakin kai, ciki har da Rwanda". 

Shugaba Emmanuel Macron tare da Shugaba Félix Tshisekedi,a Kinshasa.
Shugaba Emmanuel Macron tare da Shugaba Félix Tshisekedi,a Kinshasa. AFP - LUDOVIC MARIN

Wasu matasa goma sha biyu wadanda tuni suka yi tambarin tutocin kasar Rasha suka yi zanga-zanga a birnin Kinshasa a ranar Larabar da ta gabata don nuna adawa da zuwansa, sun sake haduwa a ranar asabar da nufin yin tattaki zuwa daya daga cikin wuraren da ya kai ziyarar. Nan da nan ‘yan sanda suka tarwatsa su, aka kama shugabanninsu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.