Isa ga babban shafi

'Yan tawaye sun kashe mutane 40 a Jamhuriyar Congo

Wasu da ake zargin 'yan tawayen kungiyar ADF ne sun kashe mutane 40 a wasu tagwayen hare-hare da suka kai gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo, kamayar yadda hukumomin yankin suka tabbatar a alhamis din nan.

Wasu daga cikin 'yan tawaye a Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo.
Wasu daga cikin 'yan tawaye a Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo. AFP - ALEXIS HUGUET
Talla

Kungiyar ADF da ke da alaka da kungiyar IS, na daga cikin manyan kungoyoyin ‘yan ta’adda da ake zargi da yanka daruruwan fararen hula a yankin gabashin Congo.

Mayakan kungiyar sun kai hari ne garuruwan Mukondi da kuma Mausa da ke lardin Arewacin Kivu, a cikin daren laraba da kuma wayewar garin Alhamis.

Wani jami’I daga yankin, Kalunga Meso ya ce ‘yan ta’addan sai da suka yiwa mutanen kawanya kafin hallaka su, inda ya ce sun kashe mutane 38 a garin Mukondi sannan suka kashe 8 a Mausa kuma dukkanin mutanen da wuka aka kashe su.

A makon da ya gabata ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi alkawarin bada tukwaicin dala miliyan biyar ga duk wanda ya bada bayanan inda shugaban kungiyar ADF Seka Musa Baluku ya ke.

Tun a shekarar 2021 ne dai tawagar sojojin Congo da kuma Uganda suka fara gudanar da sintiri a yankin gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo da zummar kawo karshen ‘yan ta’adda, amma sai dai har yanzu ana ci gaba da fuskantar barazanar hare-haren su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.