Rasha ta sallami jami'an diflomasiyyar Austria hudu
A wani matakin mayar da martani, Rasha ta sanar da korar jami’an Diflomasiyyar Austria 4 bayan kasar ta koro jami’an diflomaisyyar Moscow zuwa gida, a dai dai lokacin da alaka ke kara tsami tsakanin kasar da kawayenta na Turai tun bayan da ta fara mamayarta a Ukraine.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce an bai wa jami’an daga yanzu zuwa ranar 25 ga watan nan su fice daga kasar.
A wata sanarwa, ma’aikatar harkokin wajen Rasha ta ce sallamar jami’an diflomasiyarta da Austria ta yi mataki ne mara kyau da ya haddasa tsamin dangantaka a tsakaninsu.
Austria da sauran kasashen kungiyar Turayyar Turai ta salami gwamman jaami’an diflomasiyar Rasha tun bayan da ta kaddamar ad mamaya a kan Ukraine, a yayin da Rasha ke daukar matakan ramuwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu