Isa ga babban shafi

Dakarun Rasha na gwabza fada da na Ukraine a yankin Bakhmout

Shugaban kungiyar Wagner ya tseguntawa manema labarai cewa mummunan fada na gudana a yankin Bakhmout, a gabashin Ukraine, tsakanin dakarun Rasha da sojojin Ukraine, yayin da mutane biyar suka jikkata a harin da Rasha ta kai kan Kharkiv, birni na biyu na kasar Ukraine.

Birnin Kharkiv na kasar Ukraine
Birnin Kharkiv na kasar Ukraine © REUTERS/Vitalii Hnidyi
Talla

Shugaban rundunar sojojin Rasha, Evguéni Prigojine, wanda mutanensa ke kan gaba a fagen daga ya tabbatar da kokarin da dakarun sa ke yi a wannan yaki yankunan arewa na Bakhmout.

 "Rundunar sojin Ukraine ba ta ja da baya. Suna fafatawa har zuwa mutum na karshea cewar Evguéni Prigojine, kamar yadda kafar yada labaransa ta Telegram ta ruwaito.

Babban hafsan sojin Ukraine ya tabbatar ba tare da yin cikakken bayani kan fada da tashin bama-bamai da ake ci gaba da yi a wurare da dama a gabashin kasar inda sojojin Rasha suka samu kananan nasarori a cikin 'yan makonnin nan.

A birnin Kharkiv da ke arewa maso gabashin kasar, hukumomi sun ba da rahoton wasu hare-hare biyu na Rasha da suka yi da suka jikkata akalla biyar tare da lalata gine-ginen.

A cewar ofishin mai shigar da kara na yankin, wanda kuma ya bayar da rahoton jikkata biyar, sojojin Rasha sun harba makami mai linzami na S-300 guda biyu a birnin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.